ABNA24 : Tashar talabijin ta al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa mayakan kungiyar Taliban sun mamaye wasu garuruwan ba tare da wata turjiya daga bangaren sojojin gwamnatin kasar ba.
Labarin ya kara da cewa shugaban kasar ta Afganistan Ashraf Ghani ya bukaci mayakan kungiyoyi wadanda ya yi ta samun sabani da su a baya, da su taimaka don kare babban birnin kasar Kabul daga fadawa hannun Taliban.
Wasu mutanen kasar sun bayyana cewa mayakan Taliban sukan kwace manya manyan gine-ginen hukumomin kasar a duk lokacin suka shiga wani gari.
342/